Search
Close this search box.

Gaza: Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada Ya Haura 32,000

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta ce Adadin wadanda su ka yi shahadi sun kai 32, da 975, wadanda suka jikkata kuma sun kai 75,000

Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta ce Adadin wadanda su ka yi shahadi sun kai 32, da 975, wadanda suka jikkata kuma sun kai 75,000 da 577. Kaso 70 % na wadanda su ka yi shahadar da kuma jikkata mata ne da kananan yara.

Har ila yau wannan sanarwar ta ce; A halin yanzu da akwai wasu Falasdinawan da adadinsu ya kai 8000 da ke karkashin baraguzai, kuma rashin kayan aiki ya sa ba za aiya fito da su ba.

Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba ne dai sojojin HKI su ka fara kai wa yankin Gaza hare-hare ta sama, kasa da ruwa, a karkashin cikakken goyon bayan kasashen turai da kariya da kuma taimakon Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments