Search
Close this search box.

Gaza : Adadin Falasdinawan Da Isra’ila Ta Kashe Ya Kai 40,476

Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 40,476 a yakin kisan kare-dangi da ta kwashe watanni 11 tana yi a Gaza, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta

Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla 40,476 a yakin kisan kare-dangi da ta kwashe watanni 11 tana yi a Gaza, a cewar Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta yankin.

Adadin ya hada da mutum 41 da jiragen yakinta suka kashe a awa 24 da suka wuce, a cewar sanarwar da ma’aikatar ta fitar. Ta kara da cewa Isra’ila ta jikkata mutum 93,647 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba da ta kaddamar da yaki a yankin.

Ko a baya bayan nan Isra’ila ta kashe Falasdinawa akalla shida a Birnin Gaza na yankin Falasdinu bayan jiragen yakinta sun kai hari wani gida.

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari a sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi, inda suka kashe Falasdinawa akalla uku, ciki har da jariri, tare da jikkata wasu, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA.

Ya kara da cewa jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa sun gano gawa uku tare da mutanen da suka jikkata bayan Isra’ila ta yi luguden wuta a wani gida na iyalan Na’san a Layin Yermouk na Birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments