Garib Abadi: Iran Ba Za Ta Shiga Wata Tattaunawa A Cikin Halin Rauni Ba

Jami’i mai kula da harkokin dokokin kasa da kasa a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran, Kazim Garib Abad, ya bayyana cewa; Babu yadda

Jami’i mai kula da harkokin dokokin kasa da kasa a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran, Kazim Garib Abad, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta shiga duk wata tattaunawa a cikin halin rauni.”

A wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida, Garib Abadi ya ce, bayan harin kwanaki 12 na HKI akan Iran, muna da matsayar da mu ka dauka akan batun tattaunawa, wacce har yanzu ita ce ake aiki da ita. Wannan matsayar kuwa ita ce wajibi ne a kare, hakkokin Iran a fagen makamashin Nukiliya da dauke takunkumai, da su ne abubuwan da za a mayar da hankali akansu a cikin duk wata tattaunawa.”

Garin Abadi ya kuma ce; Babu yadda za a yi mu aminta da banagren da za a tattauna da shi, za kuma mu ci gaba da zama a haka. Haka nan kuma a kodayaushe za mu ci gaba da kasantuwa cikin Shirin fuskantar kowane irin yanayi.”

Garib Abadi ya kara da cewa: Zama akan teburin tattaunawa ba za sa sojoji su saki jiki cewa babu abinda zai faru. Ko kadan haka ba za ya faru ba, za su kasance a cikin shiri. Ana tattaunawa, kuma sojojin suna cikin Shirin mayar da martani akan kowane irin wuce gona da iri. Babu cin karo a tsakaninsu.”

 A gefe daya, ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa; Amurka ta aiko wa Iran da sakwanni mabanbanta akan cewa tana son a koma tattaunawa.”

Haka nan kuma ya kara da cewa; Iran tana yin nazarin sakwannin na Amurka domin bayar da martani akan inda za a yi tattaunawar da kuma yadda za ta kasance, haka nan kuma abubuwan da za ta kunsa.”

Abbas Arakci ya ce, Iran ba ta gaggawar sake kumawa cikin tattaunawar da ba ta yi nazarinta ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments