Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Yi Dirar Mikiya Kan Fira Ministan Gwamnatin Mamayar Isra’ila

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi dirar mikiya kan Netanyahu a matsayin mai laifin yaki da ke ingiza Amurka kan yaki da Iran Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya soki fira ministan gwamnatin Isra’ila Benjamin Netanyahu, inda ya nuna shakku kan harkokin siyasarsa da kuma dangantakarsa da Amurka. Yana tambayar cewa; Mene ne […]
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran Ya Yi Gargadi Kan Sake Kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Iran ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskuren kai hari kan Iran, lallai zasu fuskanci mayar da martani da karfi Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdurrahim Mousawi ya jaddada cewa: Idan makiya suka sake yin kuskure to za su fuskanci martani mai radadi da karfi da […]
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Gargadi Kan Batun Sake Kakaba Mata Takunkumi

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Kunna wutar tayar da hankali, zata fuskanci martani da ya dace da ita daga kasar Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Abin da ake kira na’urar tayar da hankali ba shi da wani tushe na doka, komawa zuwa irin wannan tsarin ba […]
Kungiyar Ba Da Agaji Ta Red Crescent Ta Iran Ta Bayyana Yawan Kananan Yara Da ‘Yan Sahayoniyya Suka Kashe A Iran

Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta bayyana cewa: Yaran Iran 41 ne suka yi shahada a lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai hari kan kasar Iran Shugaban kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Iran Pirhossein Kolivand ya tabbatar da cewa; Barnar da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi kan Iran ita […]
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Likita A Hare-Haren Da Suka Kai Kan Zirin Gaza

Wani kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila ta kai ya kashe wani fitaccen likita da fararen hula a Gaza Dr. Ahmed Qandil, mai ba da shawara kan aikin tiyata da Sanya ido a asibitin Baptist, ya yi shahada a jiya lahadi, tare da wasu mutane 17, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wani […]
Ma’aikatan Kwana Kwana 5 Ne Suka Yi Shahada A Yakin Kwnaki 12 Da HKI Da Amurka

Pir-hossein Kolivand, shugaban hukumar kwana-kwana ko kashe gobara na kasar Iran wato RED Cressen ya ce ma’aikatansa 5 ne suka rasa rayukansu a lokacinda suke aiki a cikin yakin kwanaki 12 da HKI a duk fadin Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Pirhossein Kolivand yana fadar haka a safiyar yau litinin […]
Jakadun Kasashen Waje Sun Ziyarci Ginin IRIB Da HKI Takaiwa Hare A Yakin Kwanaki 12

Jakadun kasashe 28 ne a nan Tehran suka kai ziyarar ginin ido ga ginin hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a jiya Lahadi, inda suka yi All..wadai da hakan suka kuma bayyana cewa wannan kokarin ruwa bakin yan jarida ne wadanda suke fadin gaskiya. Kamfanin dillancin laraban IP na kasar Iran ya nakalto jami’an […]
Burtaniya, Faransa Da Jamus Sun Kaskantar Da Kansu A Lokacinda Suka Goyi Bayan Hare-Haren HKI Kan Iran

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan harkokin sharia da kuma kasa da kasa ya ce kasashe uku na turai Burtaniya da Faransa da kuma Jamus sun kada mutuncinsu a lokacinda suka giye bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka dorawa JMI. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazen Gharibabadi […]
EU Ta Ce Zata Maida Martani Kan Amurka Da Kudaden Fito Na Euro Biliyon 21 Tare Da Yiyuwan Kari

Kungiyar tarayyar Turai UE ta bada sanarwan cewa ta shirya tsab don amidawa gwamnatin Amurka martani na kudaden fito mai yawan Euro billion 21, tare da yiyuwan kara shi, a matsayin martani ga kasar ta Amurka na karin kudaden fito na kasha 30% kan kasashen kungiyar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto […]
Garib Abadi: Iran Ba Za Ta Shiga Wata Tattaunawa A Cikin Halin Rauni Ba

Jami’i mai kula da harkokin dokokin kasa da kasa a ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran, Kazim Garib Abad, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta shiga duk wata tattaunawa a cikin halin rauni.” A wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta cikin gida, Garib Abadi ya […]
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari Ya Rasu Yana Dan Shekaru 82

A jiya Lahadi ne mai Magana da yawun shugaban kasar Najeriya, Bola Tinibu ya rubuta a shafinsa na X cewa; Shugaba Buhari ya rasu a yau, a birnin London da misalin karfe 4;30″ A shekarar 2015 ne dai shugaba Buhari ya zama dan takara na farko wanda ya yi nasara akan shugaban kasar da yake […]
An Daure Mutane 44 Tare Da Aiki Mai Tsanani Saboda Taimaka Wa Boko Haram Da Kudi

Hukumar da take fada da ‘ta’addanci a Najeriya, ta sanar da daure mutane 30 da aka samu da laifin taimaka wa kungiyar Boko Haram da kudade,yayin da aka dage shari’ar wasu 10 zuwa wani lokaci anan gaba. An yi zaman shariar ne dai a wasu kotuna 4 na musamman da aka kafa, a cikin barikin […]
Fiye Da Falasdinawa 100 Ne Su Ka Yi Shahada A Jiya Lahadi

Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa adadin mai yawa na Falasdinawa sun yi shahada, saboda ci gaba da kai hare-haren ta’addancin HKI a yankuna mabanbanta. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta nakalto majiyar Falasdinawa tana cewa; Falasdinawa fiye da 100 su ka yi shahada a sanadiyyar harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai a yankunan mabanbanta […]