Kasashen gungun G7 sun ba da sanarwar cewa za su mutunta wajibcin da ya rataya a wuyansu dangane da sammacin kame da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta bayar kan Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
“Muna nanata kudurinmu ga dokokin jin kai na kasa da kasa kuma za mu mutunta nauyin da ke wuyanmu,” in ji manyan suka fitar bayan wani taro a Rome.
Amurka dai bata cikin kasashen da suka amince da kotun ta ICC, kuma ta bayyana sammacin na kotun ga manyan jami’an na Isra’ila a matsayin abun kunya da kuma kin jinin yahudawa.
A ranar Alhamis data gabata ce kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta bayar umarnin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yakinsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da suka aikata a Gaza.
Bisa ga umarnin kotun ICC, ana gurfanar da wadanda suka aikata laifukan yaki a kasashe mambobin kotun 120 wadanda kuma tilas su kama firaministan na Isra’ila da tsohon ministan yakinsa a lokacin da suka isa kasashen.