Wasu masana suna ganin shirin abinda ya faru da jirgin fasinja Flydubai wani shiri ne firay ministan HKI Benyamin Natanyahu na sake jawo Amurka cikin yaki da JMI ne, sannan na ci gaba da shugabancin gwamnatin HKI.
Tashan talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a cikin yan kwanakin da suka gabata ne Natanyahu ya kai ziyara UAE a asirce inda ya gana da Mohammad bin Zayed. Don haka mafi yawan zato itace sun shirya hatsarin Flydubai ne don cimma wata manufa ko manufofi kan JMI da kuma samar da wani yanayi a HKI wanda zai bawa Natanyahu damar dage zabubbuka wanda za’a gudanar a ranar 27 ga watan Octoban da muke ciki.
Labarin ya kara da cewa kafin haka Abu Dhabi ya bawa Natanyahu labarin cewa wai kungiyar Hamasa tana shirin kaiwa HKI hare hare a dai dai lokacinda 7 ga watan Octoba yake karatowa.
A ranar laraba ce wani jirgin Fasinja Flydubai kirar Boeng 737 dauke da fasinjoji 174 mafi yawansu yahudawa yan share wuri zauna yan mamaya daga Abudhabi zuwa kasar mamaya sai wai kamar yanda suka fada rikici tsakanin matuka jirgi biyu ya tashi har dayan ya kashe daya. Wanda ya tilsatawa jirgin sauka a yankin tabuka na kasar Saudia kafin wani jirgin ya karasa da su zuwa cikin HKI.
Yahudawan Musamman Natanyahu sun dorawa JMI laifi kan wannan abinda ya faru amma masu bincike a kasar Saudia basu tabbatar da hakan ba. Daya daga cikin matuka jirgin mutumin kasar Omman ne, suna kuma zargin yana goyon bayan JMI, shi yasa ya tada hankali a jirnin don kashe yahudawan sahyoniyya.