Cibiyar Kididdiga Ta HKI ta fitar da alkaluma da suke nuni da cewa ‘yan sahayoniya da dama ne su ka gudu zuwa waje,tare da bayyana cewa mazauna Tel Aviv ne suke kan gaba wajen yin hijirar.
Kididdigar ta kuma bayyana cewa, bayan Tel Aviv, birni na biyu dake binsa na masu yin hijirar shi ne Haifa.
Rahoton ya kuma kara da cewa yakin Gaza da kuma Lebanon ne sanadiyyar yin hijirar yahudawa ‘yan share wuri zauna din a 2024 da adadinsu ya haura 11,000.
Daga Tel Aviv adadin masu yin hijirar sun kai 11,000, daga Haifa kuma wadanda su ka yi hijirar sun kai 6,000, sai kuma wani adadin da ya kai 5,370 daga garin Nataniya, haka nan kuma wasu 5,000 daga birnin Kudus.
Jaridar “Yediot Ahranot” ta ce wannan adadin na masu yin hijira ya haifar da damuwa saboda masu yin hijirar shekarunsu ba su wuce 45.
Tun da aka fara yakin Gaza ne dai yahuwa ‘yan share wuri zauna su ka fara ficewa daga HKI zuwa kasashen turai, yayin da wasu ke rabuwa da takarudun zamansu ‘yan “Isra’ila” baki daya.