Majiyar asibiti ta fada wa kafafen watsa labaru cewa; Tun daga safiyar yau Talata ne HKI ta fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta dake Arewacin Gaza wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama.
A yankin Khan-Yunus adadin shahidan Flasdinawa sun kai 5, sai kuma wasu 3 a yankin Bait-Lahiya.
Mazauna unguwar Sheikh Ridhwan sun ce jiragen yakin HKI sun rika kai hare-hare a jere a yau Talata.
A kudancin yankin Gaza jirgin saman HKI na yaki ya kai hari akan wani gini mai hawa 4 da hakan ya yi sanadiyyar zubewarsa akan mutanen da suke ciki. An sami shahidai da ba a kai ga tantance yawansu ba, zuwa yanzu.
A titin al-Jala’a da yake a cikin birnin Gaza, wani mutum daya ya yi shahada, kamar yadda tashar talbijin din aljazira ta ambata.