Rahotanni daga Gaza sun ambaci cewa adadin mai yawa na Falasdinawa sun yi shahada, saboda ci gaba da kai hare-haren ta’addancin HKI a yankuna mabanbanta.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta nakalto majiyar Falasdinawa tana cewa; Falasdinawa fiye da 100 su ka yi shahada a sanadiyyar harin da ‘yan sahayoniyar su ka kai a yankunan mabanbanta na Gaza.
Daga cikin yankunan da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa hare-hare da akwai ‘Maslakh’ dake kudancin Khan-Yunus, a lokacin da Falasdinawa suke jiran samun taimakon kayan abinci.
A kudancin yankin Gaza an sami shahidi daya da kuma wasu 20 da su ka jikkata, sai kuma wasu 10 da aka raunata a Khan-Yunus,daga hari da jirgi maras matuki da HKI ta kai wa sansanin ‘yan hijira a Qadisiyya.
A unguwar “Zaytun” ma mutum daya ya yi shahada sai kuma wasu mutane biyu da su ka raunata.
Hukumar dake aikin ceto a Gaza, ta sanar da cewa daya daga cikin ma’aikatanta ya yi shahada, yayin da wani daya ya jikkata.
Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wurin da Falasdinawa su ka shiga layi domin dibar ruwan sha, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu.
Wani wurin da sojojin HKI su ka kai wa harin ta’addancin da akwai kasuwar da take cike da mutane makil da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 17.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta ce, daga cikin wadanda su ka yi shahada a jiya Lahadin da akwai fitaccen likita Ahmad Qandil.