Fitar Da Kayayyaki Daga Afirka Ya Karu Da Kashi 14%

Hakan ya sanya Afrika ta biyo bayan Asiya a cewar wani rahoto da Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) ta fitar
Fitar da kayayaki daga Afrika

Fitar da kayayyaki daga Afirka ya karu da kashi 14% a kwata na farko na 2026, duk da yakin da aka yi a Gabas ta Tsakiya, Kwatankwacin karuwar kashi 25% tun daga 2023.

Hakan ya sanya Afrika ta biyo bayan Asiya a cewar wani rahoto da Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) ta fitar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin danyen mai na Brent ya tashi, inda ya kai matsayi mafi girma tun 2022, saboda karuwar yakin Amurka da Iran da kuma rufe mashigin tekun Hormuz.

Ci gaban na Afirka ya samo asali ne daga fitar da karafa masu daraja, zinare, jan karfe, takin zamani, da ma’adanai, duk da raguwar fitar da koko da man fetur.

Duk da haka, wannan yanayi yana nuna ci gaba da dogaro da nahiyar kan fitar da kayan masarufi.

Tashin  farashin zinare, a lokutan rikici, wanda ya tashi da kashi 40% a shekarar 2025, ya zama babban alheri ga kasashe kamar Afirka ta Kudu, babbar mai samar da karfe mai daraja a Afirka, wadanda suke amfana sosai daga hauhawar farashi.

A bangaren takin zamani, Morocco ta kuma sami riba daga fitar da sinadarin phosphates, wanda farashinsa ya tashi sosai a duniya a daidai lokacin da ake samun cikas a samar da kayayyaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted