Fira Ministan kasar ta Qatar Muhammad Bin Abdur-rahman ali-Thani zai iso nan kasar Iran a kokarin lalubo hanyoyin rage halin yaki a wannan yankin.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen na kasar Qatar Majid Ansari ya ce; daga cikin batutuwan da fira ministan zai tattauna da mahukuntan Iran da akwai bude mashigar Ruwan Hurmuz da kuma samar da yanayin komawa kan tebrun tattaunawa.
Shi kuwa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce, ziyarar ta fira ministan Qatar tana a matsayin shiga tsakanin ne a tare da Pakistan domin ci gaba da aiki da hanyoyin diplomasiyya. Haka nan kuma bangarorin biyu za su tattauna halin da ake ciki a wanann yankin na yammacin Asiya.