Ana ci gaba da farautar matukin jirgin yakin Amurka da Iran ta kakkabo

Iran ta yi tanadin tukuici mai tsoka ga duk wanda ya cafko mata matukin jirgin yakin Amurka da sojojin kasar suka kakkabo a kasar.

Kawo yanzu Amurka da iran suna ta farautar matukin jirgin yakin samfarin F15-E da aka kakkabo a sararin samaniyar tsakiyar iran.

Gidan talabijin na iran ya nuno tarkacen jirgin da iran ta kakkabo, kuma gwamnatin kasar ta umurci mazauna yankin da su bada duk wani labara game da matukin jirgin da kuma kasancewar sojojin Amurka a yankin.

Tunda farko ta sanar da kakkabo wani jirgin yakin na Amurka samfarin F35 wanda ta ce ya nutse a teku, sannan kuma wani harin ta ya shafi wasu jiragai marasa matuka biyar na Amurka.

Amurka ta sanar da cewa ta ceto daya daga cikin matukan jirgin, yayin da ta ke ci gaba da neman ceton gudan.

Haka kuma Amurka ta ce ta ceto wani matukin wani jirgin samfarin A-10 da iran ta kakkabo a kusa da mashigar ruwa ta Hormuz.

Kafofin yada labaren Amurka sun rawaito kakkabo jirgin yakin na Amurka kuma sun ce an yi wa shugaban kasar Donald Trump bayyani akan halin da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted