Hukumar (FIFA) ta bayyana cewa kasar da ta yi nasara a Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2026 za su samu tukwuicin dala miliyan 50, wanda yake wani bangare na kudin da aka ware a gasar na dala miliyan 655, wannan ya nuna karuwar kusan kashi 50 cikin 100 idan aka kwatanta da dala miliyan 440 da aka raba wa kasashe a Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2022 a Qatar.
Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, wadda za a yi daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga Yuli na shekarar 2026, a kasashen Amurka, Mexico, da Kanada, za ta kasance ta farko da za ta kunshi kasashe 48, idan aka kwatanta da 32 da suka buga gasar a baya,
A gasar da ta gabata, Hukumar Kwallon Kafa ta Argentina ta sami dala miliyan 42 bayan Lionel Messi ya jagorance su zuwa ga nasara a kan Faransa a bugun fenariti, yayinda Faransa, wacce ta zo ta biyu, ta sami dala miliyan 30.
A shekarar 2026, wadanda suka yi rashin nasara a wasan karshe za su samu dala miliyan 33, wadanda suka zo na uku kuma za su samu dala miliyan 29, sauran wadanda suka zo matakin na kusa da na karshe za su sami dala miliyan 27, kasashen da aka fitar a matakin rukuni za su sami dala miliyan 9, yayin da dukkan kasashe 48 da suka shiga gasar za su sami kyautar dala miliyan 1 da rabi a matsayin kudin shirye shirye.
Jam’ian Yan Sanda A Birtaniya Nun Kama Wasu Masu Rajin Kare Hakkin Falasdinu Guda 11 Saboda Rera Taken Intifada
Rahotanni sun bayyana cewa jamian yan sandan Birtaniya sun kama mutane 11 masu nuna goyon bayan alummar falasdinu a garuruwa daban-daban na kasar bayan da suka rera taken intifada a lokacin zanga-zanga, wanda haka ke nuna irin yadda ake take hakkin bayyana albarkacin bakin.
Haramcin furta kalma guda acikin jamaa a lokacin zanga-zanga yana sanya alamar tambaya game da takaita hakkin furta albarkacin baki, jami’an tsaron gwamnatin birtaniya sun dauki mataki kan masu zanga-zanga nuna goyon bayan falasdinawa , matakin da ya haifar da rikici tsakanin magoya bayan yahudawa da kuma masu adawa da su,
Yan sanda a birntaniya musamman a Manchester sun sanar da cewa yin amfani da Kalmar Intifada ko kuma daga wani allo dake tallata Kalmar haramun ne, wannan sanarwar ta sa aka kama mutane da dama ,Kuma ya fuskanci suka mai tsakanin daga magoya baya da masu sukar wannan tsari.
Iran da Rasha Sun yi Watsi Da Kasancewar Sojojin Ketare A Yankin Kafkaz
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a yayin tattaunawarsa da takwaransa na kasar Rasha ya bayyana cewa tabbatar da tsaro a kafkaz da tsakiyar Asiya ya doru ne a wuyan kasashen yankin, don haka basu yarda wani daga wajen ya tsoma baki cikin harkokinsu ba.
Yankin Kafkas ya zama cibiyar gasar siyasa a tsakanin kasashen dake fama da rikici tsakanin Rasha da Nato da Turkiya da kuma kasashen yankin, don haka nuna rashin amincewar iran na shigar da sojojin kasahen waje alama ce ta kokarin iran na tsara tsaron yankin tare da Mosko da kuma dakile tasirin kasashen yamma a kusa da iyakokinta na Arewa.
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro a kafkaz da tsakiyar Asiya kasashen yankin ne ya kamata su samar da shi, ba tare da tsoma bakin wani daga waje ba, wanda haka ya nuna afili cewa iran tana adawa da kasancewar sojojin ketare a yankin na kafkas kuma ta isar da matsayinta ga makwabta da kuma kawayenta.
Haka zalika yace iran da rasha sun yi tarayya da fahimtar juna kan wannan batun , inda dukkan bangarorin biyu suka yi watsi da batun shigar wani karfi daga wajen a yankin wajen samar da tsaro a kafkaz.
Falasdinawa 17 Ne Suka Mutu A Gaza Saboda Tsananin Sanyi Da Kuma Hana Shigar Da kayan Agaji Da Israi’la Ta yi
Rahotanni sun bayyana cewa yanayin sanyi mai tsanani da aka shiga a yankin gaza yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa da dama,a cikin wannan watan kamar yadda majiyoyin labaran yankin suka bayyana, adadai lokacin da Isra’ila take ci gaba da hana shigar da kayayyakin agaji da suka hada da Haimomi da sauran abubuwan bukatun rayuwa na yau da kullum.
Hukumar kare fararen hula a yankin gaza ta bayyana cewa akalla mutane 17 sun rasa rayukansu a cikin watan decemba saboda ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya da kuma iska mai tsanani da sanyi kamar kankara da ya mamaye sansanin yan gudun hijira da hakan ya haddasa rugujewar katangar gidaje da kuma tanti, wanda dama daga ciki sun lalace saboda hare haren da isra’ila ta kai.
Kakakin hukumar mahamud basal ya bayyana cewa yanayi sanyi yana kara tsananta musamman da dare, don haka yayi gargadin cewa tsananin sanya yana barazana ga rayuwar yara kanana saboda karancin matsugunnai da abin dumama jiki,
Yace abin da ke faruwa yanzu haka a Gaza shi ne babban balain da dan Adam ke fuskanta don haka yayi kira da a cece rayuwar yara kanana tun kafin sanyi ya gama da su, yace kuma wannan yana zuwa ne saboda kin cika alkawarin da isra’ila ta dauka a yarjejeniyar da aka cimma ta tadakatar da bude wuta a 10 ga watan Oktoba .
Shugaban Kasar Iran Ya Gargadi Amurka Kada Ta yi Amfani Da Tattaunawa Don Raunan Iran Kan Isra’ila
Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Tehran ba za ta taba amincewa da sharuddan kasantarwa ba don tattaunawa da Amurka, yana gargadi game yunkurin kwace karfin sojan iran da kuma raunanta akan gwamnatin Isra’ila.
Da yake Magana da manyan jami’an gwamantin da manyan yan siyasa a jiya laraba prezeshkiyan yace: iran ta tattaunawa da kasar Amurka har aka kusa cimma matsaya, amma sai ta lalata tattaunawar ta hanyar kaddamar da yaki akanta a tsakiyar watan yuli,
Har ila yau ya nanata cewa iran ba ta neman rigima da kowa ,kuma ta sha sanar da cewa bata son kera makamin nukiliya, kuma a shiye take a gudanar da duk wani aiki na tantancewa.
Amurka ta sanya wasu sabbin sharudda don fara sabuwar tattaunawa da Iran, tana so iran ta dakatar da tace yuraniyom baki daya, kuma ta rage kera makami mai linzami, sai dai tuni Tehran tayi watsi da wadannan sharudda tare da bayyana su a matsayin take hakokin alummar kasar ta ne.