Ficewar Amurka Daga Iraki Manuniya Ce Ta Ficewarta Daga Asiya

ficewar sojojin Amurka daga iraki daidai yake da sansanin ficewarta daga kasashen musulmi

Dakatarun kare juyin musulunci na kasar iran sun bayyana cewa ficewar dakarun sojin Amurka daga  kasar iraki wata alamace ta fara ficewar su daga yammacin asiya da kuma sauran kasashen musulmi,

Dakarun na IRGC sun fitar da wannan bayani ne a yau Alhamis kwana daya bayan da sojojin Amurka suka fice baki daya daga kasar Iraqi , wanda ya kawo karshen mamayarsu na tsawon shekaru 23 suna mamaye da kasar ta larabawa da ya kai ga mutuwar dubban daruruwan fararen hula haka siddan

Haka zalika sun kara da cewa Amurka ta dauki lokaci tana amfani da yaren nuna fin karfin soji, amma yanzu ta fice baki daya daga kasar da ta mamaye da karfin tsiya na gwamman shekaru , kuma sun bayyana ficewar sojojin Amurka a matsayin wata shaida na tsayin Dakar irakawa wajen tunkarar yan ta”adda da  kasar Amurka ‘yar ina da yaki da kuma sauran shuwagabanninta  dake fadar white house

Daga karshe kungiyar ta IRGC tace korar sojojin Amurka daga iraki matakin farko ne na daukar fansar jinanan shahidan iraki, musamman abu Mahdi al-muhandis mataimakin kwamandan rundunar popular mobilization units ta iraki wanda aka kashe tare da babban kwamandan iran mai yaki da ta’addanci laftanar janar Qaseem Sulaimani a wani hari da Amurka ta kai a bagadaza a shekara ta 2020

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted