Dubai: Fashewar Wasu Abubuwa Ya Haifar DaGobara

Rahotonni sun bayyana cewa: An ji fashewar wasu abubuwa da tashin gobara mai tsanani a Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Wasu majiyoyin watsa labarai

Rahotonni sun bayyana cewa: An ji fashewar wasu abubuwa da tashin gobara mai tsanani a Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

Wasu majiyoyin watsa labarai na Larabawa sun watsa rahoton cewa: An ji fashewar wasu abubuwa masu karfi tare da tashin gobara a yankin kasuwanci da masana’antu na tashar jiragen ruwa ta Jebel Ali da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Tasnim News Agency, majiyoyin Larabawa sun ba da rahoton fashewar abubuwa akalla bakwai a tashar jiragen ruwa ta Jebel Ali da ke birnin Dubai a safiyar yau Laraba a yanki da ake ganin cibiyar kasuwanci da masana’antu ce ta masarautar.

Ba a fayyace yanayin lamarin ba a lokacin rubuta wannan rahoto, kodayake wasu ma’aikata da suke aiki a wurin sun ce an gano wani abu da ya haifar da fashewar, wanda gobara ta biyo baya tare da bullar hayaki da ya tirnike yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted