Fasfon Kungiyar AES, Zai Fara Aiki A Karshen Watan Janairu

Kungiyar hadakar kasashen nan uku na da sojoji ke mulki wato AES ko Sahel Alliance ta sanar da cewa fasfon kungiyar zai fara aiki a

Kungiyar hadakar kasashen nan uku na da sojoji ke mulki wato AES ko Sahel Alliance ta sanar da cewa fasfon kungiyar zai fara aiki a ranar 29 ga Janairun shekarar 2025 din nan.

Shugaban kungiyar ta AES Assimi Goita ne ya sanar da hakan a wata sanarwa ta musamman da aka fitar a jiya.

Sanarwar ta ce duk da cewa sabon fasfon zai fara aiki daga 29 ga Janairun 2025, masu tsohon fasfo wanda ke da tambarin ECOWAS na da zabin su ci gaba da amfani da fasfon su har zuwa lokacin da wa’adinsa zai kare ko kuma za su iya zuwa a sauya musu sabon fasfo mai dauke da tambarin AES.

“A wani bangare na aiwatar da manufofi, musamman abubuwan da suka shafi shige da fice, shugaban kungiyar na sanar da kungiyoyin tarayya da na kasa da kasa game da fara aikin fasfo na AES, daga ranar 29 ga Janairu, 2025,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kasashen kungiyar da ta hada Mali, Nijar da Burkina faso sun sanar da ficewa daga kungiyar ta Ecowas bayan juyin mulkin da sojoji sukayi daya baya daya suna masu zargin kungiyar ta ECOWAS da zama ‘yar amshin shatan kasashen yamma musaman faransa da ta yi musu mulkin mallaka.

Baya ga hakan sun shiga takun tsaka da kungiyar da ta yi barazanar abkawa Nijar da karfin soji bayan juyin mulkin da sojoji sukayi wa Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments