Farashin Man Fetur Samfurin “Brent” YA Haura Dala 10 Kowace Ganga Daya

Farashin Man Fetur Samfurin "Brent" YA Haura Dala 10 Kowace Ganga Daya
hauhawar farashi

A yau Laraba ne aka sanar da cewa farashin kowace ganga daya ta man fetur samfurin “Brent” da aka yi yarjejeniyar mika wa masu saye a nan gaba, ya haura dala 100. Wannan shi ne tashin farashi mafi tsanani tun daga ranar 24 ga watan Yuli saboda yakin wuce gona da iri na Amurka akan kasar Iran.

Da misalin karfe 07: 21 na safiyar yau agogon GMT ne dai aka sami karuwar farashin da Dala 2.15, da hakan yake nufin kowace ganga ta samfurin “Brent”  kai Dala 100.7. Shi kuwa man fetur nayammacin Taxes a Amurka ya karu da dala 1.70 da kuma dala 1.83,da hakan yake nufin kowace ganga ta kama Dala 94.73.

Yakin da Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kallafawa Iran, da kuma fada a tsakanin Saudiyya da Yemen, suna cikin muhimman dalilan hauhawar farashin man fetur din a kasuwannin duniya.

Babban mai gudanar da bincike a cibiyar “Restard Energy” Claudio Gentile ya bayyana cewa; An sami raguwar yawan man fetur da yake wucewa ta mashigar Ruwan Hurmuz zuwa kasa da ganga miliyan 4.3 a kowace rana da yake a matsayin 4% na wanda ya saba wucewa.

Dama dai a cikin kwanaki biyu da su ka shude, bankin “Goldman Sachch” ya yi hasashen cewa farashin kowace ganga ta mai za ta kai wa Dala 150 idan har aka ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin tekun Pasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted