Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun DRUZHBAC Na Kasar Rasha
Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa farashin man ya tashi a jiya laraba, amma kuma tare da wannan fatan ya sake tashi.
A cikin makonnin da suka gabata ne sojojin kasar Ukraine suka kai hare-hare kan bututun man tare da amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa.
Labarin ya kara da cewa tuni kamfanonin man fetur a kasashen Slovakia da kuma Hungary sun bayyana cewa bayan katsewa na wasu yan kwanaki, man fetur ya dara kwarara daga bututun man fetur na DRUZHBA daga kasar Rasha.
A wani bangare kuma kasuwar man fetur tana jiran matakin da gwamnatin kasar Indiya zata dauka bayan da gwamnatin shugaba Trump ta karawa kayakin da ake shigo da su Amurka daga india kudaden fito na kasha 50%. Saboda Trump ya ce dole ne kasar Indiya ta dakatar da sayan mai na kasar rasha.