Hukumomin sojin Chadi sun ce kasar faransa ta mika musu sansanin soji na farko a cikin tsarin janye sojojin faransa daga kasar.
Yau Alhamis ne aka mayar da sansanin sojin Faransa da ke yankin Faya ga rundunar sojin kasar, kasa da wata guda bayan sanarwar da aka yi na dakatar da yarjejeniyar soji tsakanin Paris da Ndjamena, kamar yadda babban hafsan sojin Chadi ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Kafofin yada labarai na Chadi sun ce “Jami’an sojojin kasar za su sanar da jama’a game da ficewa daga sansanonin Abéché da Ndjamena a nan gaba, kwanaki uku gabanin zaben ‘yan majalisar dokoki, larduna da na kananan hukumomi.
Dama dai Kasar Chadi ta bukaci faransa da ta gama janye dakarunta daga kasar kafin ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2025 mai shirin kamawa.
Bayanai sun ce bangarorin na ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu game da shirin ficewar dakarun na faransa daga Chadi.
A kwanakin da suka gabata ne Kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga Chadi, inda ta fara janye wasu jiragen yakinta.
Kuma shi ne matakin farko na maida kayan aikin sojin Faransa da aka jibge a N’Djamena,”
Ana dai tattaunawa ko Faransar za ta janye sauran dakarunta 1,000 a kasar ta Chadi.
Kasar Chadi ta kasance daya daga cikin kasashen karshe da Faransa ta girke sojoji a yankin, bayan da aka kore su daga kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
A wani mataki na ba-zata ne da gwamnatin kasar Chadi ta dauka a ranar 28 ga watan Nuwamba, ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ta kulla da Faransa, inda ta bayyana hakan a matsayin wani sauyi ga kasar tare da jaddada cewa, matakin zai bai wa kasashen Afirka damar sake daidaita huldar abokantaka daidai da manufofin kasashensu.