Faransa Ta Mika Wa Chadi Sansanin Sojin Abéché

A kasar Chadi, yau Asabar ne ake san ran Faransa zata mikawa hukumomin kasar  sansanin sojin Abéché. Birnin na uku mafi yawan jama’a a kasar

A kasar Chadi, yau Asabar ne ake san ran Faransa zata mikawa hukumomin kasar  sansanin sojin Abéché.

Birnin na uku mafi yawan jama’a a kasar ya sha wahala a lokacin mulkin mallaka na Faransa, wanda ya sanya mazauna birnin ke matukar farin ciki da ganin ficewar sojojin Faransa.

Matakin dai na daga cikin tsarin aiwatar da kawo karshen yarjejeniyar hadin guiwa ta tsaro da kasar ta faransa a ranar 28 ga watan Nuwamba.

Dama tun farko faransa ta fara kwashe kayan sojojin Faransa sannu a hankali.

Bayan dai da kasashen Mali, Burkina faso da Nijar suka raba gari da faransa bayan juyin mulkin sojoji, yanzu haka suna shirin ficewa daga Chadin, Senegal, da kuma Ivory Coast.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments