Faransa ta mayar wa Netanyahu da martani kan zargin Macron da kyamr baki

Ministan Faransa a harkokin Turai, Benjamin Haddad, ya bayyana cewa babu wasu darussan da Faransa za ta dauka daga Isra’ila kan yaki da kyamar baki,

Ministan Faransa a harkokin Turai, Benjamin Haddad, ya bayyana cewa babu wasu darussan da Faransa za ta dauka daga Isra’ila kan yaki da kyamar baki, yana mai da martani kan zargin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan Shugaba Emmanuel Macron.

Da yake magana a gidan talabijin na BFMTV na Faransa, Haddad ya ce, “Ina so in fada a fili kuma da kakakusar murya  cewa wannan batu na kyamar baki, yana cutar da al’ummominmu na Turai.

Netanyahu ya zargi Macron da rura wutar kyamar baki bayan shawarar da Faransa ta yanke na amincewa da kasar Falasdinu.

Fadar Elysee ta kuma yi Allah wadai da kalaman Netanyahu da kakkausar murya, tare da bayyana furucin nasa da cewa bababn kure ne.

Faransa ta jaddada aniyar ta na yakar kyamar baki tare da tabbatar da ‘yancinta na amincewa da kasar Falasdinu a matsayin wani bangare na manufofinta na diflomasiyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted