Faransa Ta Kawo Karshen Zaman Sojojinta A Kasar Senegal

Faransa ta mika babban sansanin da sojojinta suka zauna a cikinsa na lokaci mai tsawo ga mahukuntan kasar Senegal da a can ne ta fi

Faransa ta mika babban sansanin da sojojinta suka zauna a cikinsa na lokaci mai tsawo ga mahukuntan kasar Senegal da a can ne ta fi dadewa a cikin yammacin Afirka

A jiya Alhamis ne dai aka yi kwarya-kwaryar biki na mika wa sojojin Senegal sansanin da janar Pascal Yani na Faransa ya yi a birnin Dakkar.

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce an yi kidan badujala na soja wanda ya kunshi taken kasar, sannan kuma aka sauke tutar Faransa da daga ta kasar Senegal.

Janar Yani ya ce, mika sansanin Gili da aka yi bude wani sabon shafi ne a cikin alakar sojojin. Kuma an yi hakan ne bisa bukatar gwamnatin kasar Senegal na ganin an kawo karshen zaman sojojin kasashen waje a cikin kasar.”

Janar Yani ya kara da cewa; Sojojin Faransa sun zauna a cikin Senegal fiye da karni biyu, amma sauyi wani abu ne da ya zama wajibi domin bude sabon Shafin alakar kasashen biyu.”

A shekarar da ta gabata ne dai Shugabgan kasar Senegal Basiru Faye ya bayyana cewa, ci gaba a zaman sojojin Faransa a cikin kasar, yana cin karo da ‘yancin da kasar take da shi, don haka ya zama wajibi a dauke su.”

Kasashen biyu sun cimma matsaya na kawo karshen zaman sojojin na Faransa baki daya daga nan zuwa karshen shekarar 2025 da ake ciki.

A nashi gefen babban hafsan hafsoshin sojan kasar ta Senegal Janar Mbayi Cise ya ce, sabuwar yarjejeniyar da kasashen biyu su ka cimmawa za ta kunshi bayar da horo da kuma musayar bayanai.

Sojojin Senegal suna daga cikin wadanda su ka taya Faransa fada a lokacin yakin duniya na biyu, haka nan mamayar da ‘yan Nazi su ka yi wa Paris.

Gabanin kasar Senegal, kasashe da dama na yammacin Afirka sun fitar da sojojin Faransa daga cikinsu da sun hada  Jamhuriyar Nijar, Chadi,Mali da Burkina Faso.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted