A Faransa duk da haramcin taruwa a birane da dama da kuma yawan ‘yan sanda da aka jibge, an samu fitowar jama’a sosai a fadin kasar a zanga zangar tsadar rayuwa.
Ƙungiyar Kwadaga ta CGT ta kiyasta masu zanga-zanga kusan 800,000 a duk faɗin ƙasar, yayin da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta kiyasta 410,000.
Daga Paris zuwa Toulouse, ta hanyar Bordeaux, Grenoble, Nice, da Rennes, dubban mutane sun shiga zanga-zangar.
Duk da cewa zanga-zangar a wasu sassa ta kasance cikin lumana, rikici ya barke a birane da dama, wanda ya haifar da amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zanaga.
A Paris, babban birnin kasar kungiyar CGT ta ƙidaya masu zanga-zanga 250,000, yayin da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da kuma hukumar ‘yan sandan Paris suka ƙidaya 110,000.
Rahotanni sun ce an zuba jami’an ‘yan sanda da jami’an tsaro kimanin 70,000 a faɗin Faransa, wanda ya dara na makon da ya gabata da fiye da
10,000.
Babbar kungiyar Kwadago ta CGT, ta yi tir da matakin da ta ce na hana ‘yancin yin zanga-zanga ne, hasali ma karan tsaye ne ga dimokuradiyya.
Kungiyar ta yi kira ga ma’aikata da su yi gangami a ranar 5 ga Nuwamba domin nuna fishi ga matsalar wutar lantarki da kuma kin amincewa da karin albashi ga ma’aikata.
Tuni Kungitar ta CGT ta fara tattaunawa kan shawarar shiga yajin aiki a ranar 5 ga Nuwamba.
“Lamura dai sun rincabe a Faransa bayan zanga zangar da aka gudanar a waccen Asabar wacce ta rikide zuwa tarzoma da artabu tsakanin jam’ian tsaro da masu zanga zangar kan tsadar rayuwa da hauhawan faranashin makamashi da ta samo asali daga boren daliban sakadare dake nuna fishi kan halin ko kula na gwamnatin E Macron kan sha’anin ilimi a kasar.