A faransa ana ci gaba da kira ga shugaban kasar Emmanuel Macron da ya yi murabus.
Murabus na firaminista Sébastien Lecornu ya yi, jim kadan bayan gabatar da sabuwar gwamnati, ya haifar da zaman dar-dar ga makomar Emmanuel Macron a siyasance.
Kiraye-kirayen rusa majalisa ko murabus na shugaban kasar na karuwa, yayin da jam’iyyar National Rally (RN) mai ra’ayin rikau ke kira da a gudanar da zaben wuri-wuri.
Murabus din Lecornu, wanda aka amince da shi a ranar Litinin, ya haifar da kiraye kirayen ‘yan siyasa da ke neman a rusa Majalisar Dokoki ta kasar ko kuma murabus na shugaban kasar.
Tun bayan zaben ‘yan majalisu da aka yi a shekarar 2024, babu wata jam’iyya dake da rinjaye a majlaisar, lamarin da ya jefa kasar cikin rudani ya siyasa.
A fannin tattalin arziki, harkokin Kasuwancin Paris sun fadi 3%.
Jaridun Jamus sun bayyana lamarin da barazana ga zaman lafiyar daukacin kasashen Turai.”