Faransa : An haramta wa Marie Le Pen, takara har tsawon shekaru 5

A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin

A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027.

An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi.  

An tuhumi Le Pen tare da wasu manyan yan jam’iyyar tata guda 20 da daukar masu taimaka musu aiki wadanda suka yi wa jam’iyyarta aiki maimakon Majalisar Turai wadda ita ce ke biyan ma’aikatan albashi.  

Ms Le Pen, mai shekaru 56, ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2027 ba, inda a yanzu ake ganin ita ce mafi farin jini bayan takara sau uku da ta a yi nasara ba.

Haka kuma an samu wasu ‘yan majalisar wakilai takwas daga jam’iyyarta ta (RN) da laifin wawure dukiyar jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments