Yau kwanaki 333 da fara cin zarafin bil’Adama a Gaza, kuma Falasdinawa na ci gaba da gwagwarmayar kalubalantar wannan bakar zalunci
Ayyukan wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya kan Gaza sun shiga rana ta 333, kuma babu alamun kawo karshensa bisa la’akari da rashin amincewar yahudawan sahayoniyya, da kuma shurun kasa da kasa, da kuma gazawar Larabawa.
Duk da gagarumin rushe-rushe da dimbin Falasdinawa da suka yi shahada gami da dubban wadanda suka jikkata baya ga wadanda suka bace, amma har yanzu al’ummar Gaza na ci gaba da turjuya da kalubalantar sojojin yahudawan sahayoniyya kuma ‘yan gwagwarmaya suna ci gaba da fafatawa da ‘yan mamaya a sassa daban-daban na Falasdinu.