Falasdinawa Sun Tarwatsa Tankar Yakin HKI Ta Mirkava  A Gaza

Rundunar Shahid Izzuddin al-Kassam ta tarwatsa tankar yaki samfurin “Mirkava” da kuma kakkabo jirgin  sama maras matuki na ‘yan sahayoniya a sansanin ‘Nusairat’ dake Gaza.

Rundunar Shahid Izzuddin al-Kassam ta tarwatsa tankar yaki samfurin “Mirkava” da kuma kakkabo jirgin  sama maras matuki na ‘yan sahayoniya a sansanin ‘Nusairat’ dake Gaza.

Bugu da kari  wani daga cikin mayakan na rundunar ta Kassam ya yi nasarar matsawa kusa da sojojin mamaya inda ya tarwatsa wani bom a cikinsu, da hakan ya yi sanadiyyar jikkata da kuma halakar da dama daga cikinsu

A ranar Talatar da ta gabata ma, rundunar ta Kassam ta fitar da wani faifen bidiyo da ta bai wa sunan; “Farautar macizai” da a ciki ta nuna yadda ta yi wa sojojin sahayoniyar kwanton bauna da hakan ya yi sanadiyyar halaka da jikkatar da dama daga cikinsu a gabashin “Beit-Lahiya”.

Tun a shekarar da ta gabata ne dai a ranar 7 ga watan Oktoba, HKI ta shelanta yaki akan al’ummar Gaza wanda ba komai ba ne sai kisan kiyashi da na kare dangi akan Falasdinawa. Ya zuwa yanzu fiye da mutane 45,000 su ka yi shahada yayin da wasu dubun dubata su ka jikkata. Har yanzu da akwai wasu dubban mutane da dama da suke kwnace a karkashin baraguzai da ba a kai ga fito da su ba, saboda rashin kayan aiki da kuma cigaba da kai hare-hare babu kakkautawa na sojojin  sahayoniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments