Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Alhamis

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 454, HKI tana cigaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi, inda a yau ta kai hari

A daidai lokacin da yakin Gaza yake cika kwanaki 454, HKI tana cigaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi, inda a yau ta kai hari akan hemar da ‘yan gudun hijira suke ciki a Khan-Yunus.

Tun da safiyar yau Alhamis din ne dai ‘yan mamayar su ka kai harin da ya yi sanadiyyar shahadar Falasdianwa 11, daga cikinsu da akwai kananan yara 3, da kuma jikkata wasu 12. Daga cikin wadanda su ka yi shahada din da akwai babban jami’in ‘yan sandan janar Mahmud Salah.

Har ila yau sojojin mamayar sun kai wani hari a tsakiyar zirin Gaza ta kasa da kuma ta ruwa.

A garin Deir Balah kuwa sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama masu saukar angulu wajen kai hari, haka nan kuma yankin Safdhawi dake arewa maso yammacin birnin Gaza.

Ya zuwa yanzu dai adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 45,553, sai kuma wasu 108,379 da su ka jikkata, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar.

Sai dai da akwai wasu dubban da suke a karkashin baraguzai da har yanzu ba a iya fito da su ba, saboda rashin kayan aiki da kuma cigaba da kai hare-hare babu kakkautawa a wasu yankunan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments