Jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta bayyana cewa: Fursunonin Falasdinawa 60 ne suka mutu a wuraren da ake tsare da su a haramtacciyar kasar Isra’ila saboda azabtarwa
Jaridar Wall Street Journal ta tabbatar da mutuwar fursunonin Falasdinawa da dama a lokacin da suke tsare a hannun sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila tsakanin ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa ranar 2 ga watan Yulin da ya gabata.
Jaridar ta bayyana cewa: Fursunoni 44 ne suka mutu a wuraren da ake tsare da su a barikokin sojin mamaya, yayin da wasu karin fursunoni 16 suka rasa rayukansu a gidajen yari da ake tsare da su saboda fuskantar dangogin azabtarwa.
Jaridar ta nakalto wata takarda da shugaban hukumar tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ta (Shin Bet) yayi gargadin cewa: Ka’idojin tsare Falasdinawa a haramtacciyar kasar Isra’ila na iya sabawa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan azabtarwa.
Rahoton kare hakkin dan Adam ya bayar da rahoton tabarbarewar yanayi a gidajen yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, musamman a sansanin Sasde Teman, inda aka fuskanci azabtarwa da cin zarafin fursunonin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama daga cikinsu.