Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, Falasdinawa 39,623 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila a fadin Zirin.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta kara da cewa: A cikin sa’o’i 24 da suka gabata Isra’ila ta kashe mutane 40 tare da jikkata wasu 71.
Ma’aikatar ta sanar da cewa kawo yanzu da dama daga cikin wadanda abin ya rutsa da su na a karkashin baraguzan gine-gine kuma jami’an ceto sun kasa kai musu dauki.
A halin da ake ciki MDD, ta yi kiran da a bi duk hanyoyin da suka wajaba domin kwantar da hankali.
Kiran na MDD, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar a yankin biyo bayan alawashin da Iran, da Hamas da Hezollah suka sha na mayar da martini kan kisan shugaban ofishin siyasa na Hamas Ismael Haniyah a birnin Tehran.
A wani labarin kuma shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya ce an yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kisan gilla ne da zummar tsawaita yakin Gaza da kuma dagula tattaunawar kawo karshen yakin.
“Babu tantama cewa an yi wa Mr. Haniyeh kisan gilla ne domin tsawaita yakin da kuma fadada shi,” in ji Abbas, kamar yadda ya fadawa kamfanin dilancin labaren Rasha na RIA.
“Kisan nasa zai yi mummunan tasiri a kan yarjejeniyar da ake kokaarin kullawa ta tsagaita wuta da kuma janyewar dakarun Isra’ila daga Gaza.”