Falasdinawa 38 Sun Yi Shahada A hare-haren Isra’ila

Isra’ila ta kashe Karin Falasdinawa 38 a Gaza tare da jikkata 137 a fadin Zirin a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar ma’aikatar

Isra’ila ta kashe Karin Falasdinawa 38 a Gaza tare da jikkata 137 a fadin Zirin a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin.

Kisan baya-bayan nan ya sanya adadin wadanda sukayi shahada tun a ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa 45,399, in ji ma’aikatar.

Yakin da Isra’ila ta yi a Gaza ya kuma jikkata mutane 107,940.

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta zargi Isra’ila da sanya “sababbin sharudda” a tattaunawar tsagaita bude wuta da ake ci gaba da yi da kuma jinkirta yarjejeniyar, yayin da ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zargi kungiyar Falasdinu da haifar da cikas” ga tattaunawar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments