Falasdinawa 17 Ne Suka Mutu A Gaza Saboda Tsananin Sanyi

Rahotanni sun bayyana cewa yanayin sanyi mai tsanani da aka shiga a yankin gaza yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa da dama,a cikin wannan watan kamar yadda

Rahotanni sun bayyana cewa yanayin sanyi mai tsanani da aka shiga a yankin gaza yayi sanadiyar mutuwar falasdinawa da dama,a cikin wannan watan kamar yadda majiyoyin labaran yankin suka bayyana, adadai lokacin da Isra’ila take ci gaba da hana shigar da kayayyakin agaji da suka hada da Haimomi da sauran abubuwan bukatun rayuwa na yau da kullum.

Hukumar kare fararen hula a yankin gaza ta bayyana cewa akalla mutane 17 sun rasa rayukansu a cikin watan decemba saboda ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya  da kuma iska mai tsanani da sanyi kamar kankara da ya mamaye sansanin yan gudun hijira da hakan ya haddasa rugujewar katangar gidaje da kuma tanti, wanda dama daga ciki sun lalace saboda hare haren da isra’ila ta kai.

Kakakin hukumar mahamud basal ya bayyana cewa yanayi sanyi yana kara tsananta musamman da dare, don haka yayi gargadin cewa tsananin sanya yana barazana ga rayuwar yara kanana saboda karancin matsugunnai da abin dumama jiki,

Yace abin da ke faruwa yanzu haka a Gaza shi ne babban balain da dan Adam ke fuskanta don haka yayi kira da a cece rayuwar yara kanana tun kafin sanyi ya gama da su, yace kuma wannan yana zuwa ne saboda kin cika alkawarin da isra’ila ta dauka a yarjejeniyar da aka cimma ta tadakatar da bude wuta a 10 ga watan Oktoba .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted