Sojojin mamayar HKI sun sake aikata kisan kiyashi a yankin Gaza a rana ta 422 daga fara yaki, bayan da su ka kai wasu jerin hare-hare da jiragen sama da manyan bindigogi akan Falasdinawa da suke fama da yunwa saboda karanci abinci.
A cikin sa’o’in da su ka gabata, jiragen yakin na HKI sun kai hare-hare a yankuna mabanbanta na yankin Gaza da hakan ya sa aka sami yawan shahidai da su ka kai 120 a cikin sa’oi 24.
Daga cikin yankunan da jiragen yakin HKI su ka kai wa hare-haren da akwai Khan-Yunus dake kudancin Gaza, inda ta kai hari akan sansanin da yake cike da ‘yan hijira.
Har ila yau ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a yankin al-Ammur a garin al-Fakhari.