Falasdinawa 12 Suka Mutu A Wani Sabon Hari Da HKI Ta Kai A Yankin Gaza

rahotanni sun bayyana cewa akalla falasdinawa 12 ne suka mutu yayin da wasu guda 18 kuma suka jikkata a wani sabon hari da HKI takai

rahotanni sun bayyana cewa akalla falasdinawa 12 ne suka mutu yayin da wasu guda 18 kuma suka jikkata a wani sabon hari da HKI takai a fadin yankin Gaza a cikin Saoi 24 , a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila ke yi da aka cimma tsakaninta da kungiyar gwagwarmaya ta hamas.

ministan lafiya na yankin Gaza ya bayyana cewa akalla falasdinawa guda 10 ne suka mutu a wani sabon hari da Isra’ila ta kai a yankin gaza a baya bayan nan, haka zalika an gano gawarwaki  guda 2 da suka mutu a wasu hare-haren  da isra’ila ta kai a baya.

babbar tawagar kungiyar Hamas  da kuma masu wakiltar sauran bangarorin falasdinawa sun hadu a babban birnin kasar Masar a jiya Alhamis domin tattaunawa kan sabuwar sanarwar fara aiki da matakin na biyu na yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma, duk  da ci gaba da keta yarjejeniyar da HKI ke ci gaba da yi.

tun bayan harin da HKI ta kaddamar a watan oktoban shekara ta 2023 akalla falasdinawa 71455 ne suka mutu ya yin da 171347 kuma suka jikkata bisa kididdigar baya bayan nan da hukumar lafiya ta yankin falasdinu ta fitar, yayin da falasdinawa 463 ne suka mutu daga lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta, wasu guda 1269 kuma suka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted