Fafaroma Leon na 14 ya bukaci a kawo karshen yaki a iran ta hanyar diflomatsiyya

fafaroman ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Isra’ila inda ya jadadda bukatar amfani da hanyoyin diflomatsiyya domin kawo karshen
Fafaroma Leon na 16 ya bukaci a kawo karshen yaki a iran ta hanyar diflomatsiyya

Jagoran mabiya darikar katolika ta duniya fafaroma Leon na 14 ya yi kira da a samar da hanyoyin diflomatsiyya domin kawo karshen yakin da ake da iran.

fafaroman ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Isra’ila inda ya jadadda bukatar amfani da hanyoyin diflomatsiyya domin kawo karshen yakin da ake da iran.

Kamfanin dilancin labaren IRNA, ya rawaito sanarwar fadar Vatican wadda ta rawaito tattaunawar da ta gudana tsakanin shugaban Isra’ila Isaac Herzog a ranar Juma’a inda fafaroman ya jadadda bukatar bude dukkan hanyoyin tattaunawa ta diflomatsiyya domin kawo karshen mummunan tashin hankalin da ake ciki da kuma cimma shirin zaman lafiya na hakika mai dorewa a duk fadin yankin Gabas ta tsakiya.

Fafaroman ya kuma yi kira da a kare fararen hula da kuma karfafa dokokin kasa da kasa da kuma na jin kai na duniya.
Kafin hakan dama fafaroma Leon ya yi gargadi a game da ci gaban rikicin a gabas ta tsakiya, da kuma wanzuwarsa a yankin da ma tasirinsa kan bila dama, tare da mika bukatar a kare fararen hula da kuma lalubo hanyoyin siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted