Fadar Shugaban Kasar Syria Ta Sanar Da Tsagaita Wuta A Yankin Suwaidaa

A yau Asabar fadar shugaban kasar Syria ta sanar da tsagaita wutar yaki a Suwaidaa da ta yi fama da tashe-tashen hankula. A wani bayani

A yau Asabar fadar shugaban kasar Syria ta sanar da tsagaita wutar yaki a Suwaidaa da ta yi fama da tashe-tashen hankula.

A wani bayani da fadar shugaban kasar ta Syria ta fitar ya kunshi cewa  An dauki wannan matakin ne na tsagaita wuta saboda an shiga wani yanayi mai hatsari a cikin kasar, da kuma fatan ganin an kare jinin mutanen Syria da kare hadin kan kasar da lafiyar al’ummarta, haka nan kuma saboda aiki da nauyin da ya rataya a wuya na kasa, da ‘yan’adamtaka.”

Haka nan kuma ofishin shugaban kasar ta Syria ya yi kira da a bai wa daular Syria da dukkanin cibiyoyinta da su shiga cikin yankin domin ganin an tsayar da wutar yaki.

Har ila yau ta yi kira ga dukkanin bangarorin yankin da su yi aiki da tsagaita wutar kamar yadda take, su gujewa fada da juna, da kuma kare fararen hula.

Jami’an tsaron kasar Syria sun fara shiga cikin yankuna mabanbanta domin ganin sun kare zaman lafiya a yankin.

Tun a cikin ranar 13 ga watan Yuli ne dai fada ya barke a yankin Suwaidan a tsakakin kungiyoyin ‘yan Duruz masu makamai, da kuma kungiyoyin haulolin larabawan kauye, da hakan ya yi sanadiyyar kashe mutane da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments