Fada Ya Barke Tsakanin Kungiyar M23 Da Dakarun Kasar Kongo A yau Asabar

Rahotanni daga birnin Uvira na nuni da cewa fada ya barke tsakanin kungiyar M23 da dakarun gwamnatin kasar kongo a yau Asabar 3 Janairu,2026 garuruwa

Rahotanni daga birnin Uvira na nuni da cewa fada ya barke tsakanin kungiyar M23 da dakarun gwamnatin kasar kongo a yau Asabar 3 Janairu,2026 garuruwa da dama da ke kewaye da birnin na Uvira mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo mai arzikin albarkatu, wanda ke iyaka da Rwanda da Burundi, ya fuskanci tashin hankali na tsawon shekaru 30, sai dai Lamarin ya kara tabarbarewa ne tun daga shekarar 2021 a lokacin da aka sake farfado da M23.

Bayan kwace manyan biranen gabashin biyu na Goma da Bukavu a karshen shekarar da ta gabata, kungiyar ta kaddamar da wani sabon hari a watan Disamba a lardin Kudancin Kivu kuma ta sami ikon karsbehi  a ranar 10 ga Disamba, wani birni mai matukar muhimmanci wanda ke da yawan mutane da suka kai dubu dari kusa da Burundi.

Wani mazaunin Kigongo, wanda shi ma aka same shi ta wayar tarho, ya tabbatar wa AFP cewa “rikicin ya sake barkewa da safiyar yau asabar, tare da jin karar fashewar abubuwa da harbe-harben bindiga.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted