Kungiyar tarayyar Turai tana shirin jingine aiki da HKI na wani lokacin, a cibiyoyin binciken ilmin da suke da su a nahiyar ta Turai saboda ayyukan kissan kare dangi da kuma hana abinci shiga gaza da take yi.
Tashar talabijan da Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar EU tana fadar haka, ta kuma kara da cewa kasashen turai sun gargadi HKI da ta daina hana abinci shiga gaza, amma ta yi taurine kai. Don haka a halin yanzu majalisar gudanar da na kungiyar tana shirin haramtawa HKI amfanina da wani bangare na ayyukan bincike na kasashen kungiyar, musamman wadanda suka shafi kirkirenren fasaha wato AI don kada ta yi amfani da su wajen yakar falasdinawa a gaza da ita.
Wannan shi ne karon farko wanda tarayyar Turai take daukan wani mataki, wanda shima bai taka kara ya karya ba, kan HKI.
Amma tun lokacinda aka fara yakin a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 mafi yawan kasashen turai musamman kuma kasashen Jamus da Burtania suna goyon bayan HKI, suna kuma tallafa mata da makamai don ci gaba da kissan Falasdinawa a Gaza. A yanzu al-amarin ya kaiga duniya gaba daya ta tabbatar da cewa abinda HKI take yi a Gaza kisan kiyashi ne, sai suka ce bari su yi wani abu, wanda zai zama hajjace ta kare kansu idan an ce basu yi kome ba. Amma duk da haka kungiyar tarayyar Turai tana tare da HKI 100% kan kissan Falasdinawa a Gaza.