Jagora: Iran Ta Bayyana Karfinta Da Jajircewarta A Yakin Kwanaki 12 Ga Duniya

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar mutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da […]
Mutum daya Yayi Shahada 4 Sun Ji Rauna Sanadiyar Hare-Haren HKI A Lebanon

Gwamnatin kasar Lebanon ta bada labarin cewa mutum guda ya yi shahada a yayinda, wasu mutum 4 suka ji rauni sanadiyyar hare-haren da HKI suka kai a kan gidajensu a lardin Nabatia a kudancin kasar Lebanon a safiyar a ranar Litinin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na […]
EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza

Kungiyar tarayyar Turai tana shirin jingine aiki da HKI na wani lokacin, a cibiyoyin binciken ilmin da suke da su a nahiyar ta Turai saboda ayyukan kissan kare dangi da kuma hana abinci shiga gaza da take yi. Tashar talabijan da Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar EU tana fadar haka, ta kuma kara […]
Ma’aikatar Leken Asirin JMI Ta Ce Ta Gano Shirin Kashe Manyan Mutane 35 a kasar

Ma’aikatar leken asiri na JMI ta bada sanarwan cewa ta gano shirin makiya na kashe manya-manyan Jami’an gwamnati har 35 a kasar kafin yakin da suka dorawa kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar ma’aikatar na fadar haka, ta kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 sun yi kokarin […]
Najeriya: Likitoci a Lagas Sun Shiga Yajin Aiki

Likitoci a jihar Lagos na tarayyar Najeriya sun fara yajin aiki na gargadi na kuma kwanaki 3 saboda nuna rashin amincewasu da rage hakkokinsu da kuma hanasu kudadensu wanda gwamnatin jihar take yi. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa duk tare da kokarin da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi don kada likitocin su […]
Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai

Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau […]
Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu

A cikin kwanakin bayan nan ana samun karuwar sojojin HKI da suke kashe kawunansu saboda tabuwar kwakwalensu sanadiyyar yakin Gaza. Kafafen watsa labarun HKI sun kunshi rahotanni da suke bayani akan yadda sojojin mamayar da su ka yi yaki a Gaza, suke samun tabuwar hankali, da hakan yake sa su kashe kawukansu bayan sun baro […]
Kasar Holland Ta Hana MInistocin HKI Biyu Shiga Cikin Kasarta

A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga cikinta. Kasar ta Holland ta zargi wadannan mutanen biyu da cewa suna ingiza sojojin HKI da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma fadada yawan matsugunan ‘yan sahayoniya a yankunan […]
Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba

Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo janar Musawi ya ce, ko kadan Iran ba ta yarda ko gaskata alkawullan Amurka,balle kuma zancen ‘yan sahayoniya. Babban hafsan hafsoshin sojan na Iran ya kuma kara da cewa, sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar duk wan igigi na abokan gaba. Manjo janar Musawi ya bayyana hakan […]
Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Idan aka maimaita ta’asar kai hari kan Iran, za ta mayar da martani ta hanyar da ba za a iya boyewa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani kan barazanar da jami’an Amurka suka yi a baya-bayan nan, inda ya ce idan aka sake […]
Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza. A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na […]
Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine

Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa […]
Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran

Gwamnatin kasar Faransa ta yi kakkausar suka tare da tofin Allah tsine kan harin ta’addancin da aka kai birnin Zahidan na kasar Iran Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin birnin Zahidan na kasar Iran, tare da jaddada adawar kasarta kan duk wani harin ta’addanci da aka kai kan […]
Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza

Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil […]