Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya.
Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba.
‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas.
Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.
“A lokaci guda kuma, hanyar da ta shafi bangarori daban-daban, kamar yarjejeniyar, tana da mahimmanci.
Ta ce, “Babu wata hanyar da za ta dore wajen warware matsalar sai ta diflomasiyya,” in ji ta, a cewar shafin yanar gizon EU External Action.
A kwanan ne dai shugaban AMurka Donald Trump, y ace ya aike da wasiga ga Iran, na ta bude tattaunwa ko kuma ya yi da karfin soji.
Iran dai ta musanya samun wata wasika daga Trump, kuma tana mai cewa babu batun tattaunawa bsia matsin lamba da barazana.