EU: Muna maraba da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka

Tarayyar Turai ta yi maraba da tsarin tattaunawa da ake tsakanin Iran da Amurka kuma ta jaddada bukatar ba wa diflomasiyya dama game da batun

Tarayyar Turai ta yi maraba da tsarin tattaunawa da ake tsakanin Iran da Amurka kuma ta jaddada bukatar ba wa diflomasiyya dama game da batun nukiliyar Iran.

Anouar El Anouni, babban mai magana da yawun Hukumar Tarayyar Turai, ya bayyana a wani taron manema labarai a wannan Litinin, a Brussels cewa: “Dangane da batun Iran, da farko ina so in sake nanata cewa duk wani matakin soja na iya haifar da mummunan sakamako ga zaman lafiyar yankin, yankin da tun tuni yake cikin matukar bukatar kwanciyar hankali.”

Ya kara da cewa: “Lokaci ya yi da Iran za ta nuna muhimmancinta wajen magance damuwar kasashen duniya, musamman a batun shirin nukiliyarta.”

A ranar Junar Juma’a da ta gabata ce Iran da Amurka suka koma bakin tattaunawa game da shirin nukiliyar Iran, karon farko tun bayan yakin kwanaki 12 da Isra’ila ta kaddamar kan Iran, wanda kuma ya samu goyan bayan Amurka wacce ta kai hare-haren kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted