Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD)

Gwamnatin kasar Eritrea ta bada sanarwan ficewa daga kungiyar IGAD ta raya kasashen gabacin Afrika, tare da zargin kungiyar da kaucewa daga manufofin kafata da

Gwamnatin kasar Eritrea ta bada sanarwan ficewa daga kungiyar IGAD ta raya kasashen gabacin Afrika, tare da zargin kungiyar da kaucewa daga manufofin kafata da kuma rashin tabuka wani abin a zo a gani na tabbatar da zaman lafiya a cikin kasashen kungiyar.

Kafin haka dai Adisababa tana bukatar hanya zuwa bakin tekun Redsea daga kasar Eritrea wacce ta ki amincewa, kuma hakan yana nufin mai yuwa a sake shiga yaki tsakanin kasashen biyu. Kafin haka bayan yaki na shekaru fiye da 30 an dakatar da budewa juna wuta a shekara 1993, wanda ya kare da barin Habasha ba tare da tashar jiragen ruwa a bakin tekun Rd sea ba.

Eritrea ta bar IGAD a shekara ta 2007 ta sake komawa a shekara 2023 sannan a ranar jumma’an da ta gabata ta sake ficewa karo na biyu.

Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya ce Asmara ta dauki wannan matakin ne bayan cacan baki mai zafi tsakanin ta da makobciyarta kasar Habasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted