ECOWAS za ta yi tsayin-daka domin kalubalantar juyin mulkin sojoji

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ta ce zata tashi tsayin daka domin kalubalnatar juyin mulkin sojoji. Shugaban Saliyo Julius Maada Bio,

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS, ta ce zata tashi tsayin daka domin kalubalnatar juyin mulkin sojoji.

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar a wannan karo, ya tunatar da takwarorinsa game da bukatar karfafa wannan kungiyar, wadda yanzu ta kunshi membobi 12, sakamakon ficewar membobinta uku: Mali, Nijar, da Burkina Faso.

Ya kuma jaddada cewa za a iya cimma hadin kai a yankin ne kawai ta hanyar yaki da ta’addanci kai tsaye da tsattsauran ra’ayi.

Ya kuma ce shirin kaddamar da rundunar yaki da ta’addanci mai dakaru 1,650 zuwa nan da karshen 2026,” yana kan madaidaiciyar hanya.

Haka zalika shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun yi watsi da jadawalin mika mulki da gwamnatin soja Guinea Bissau ta gabatar, kuma sun sake bukatar a dawo da tsarin mulki cikin gaggawa a kasar.

Sun kuma buƙaci a saki dukkan fursunonin siyasa da membobin kungiyoyin farar hula da aka tsare tun bayan dakatar da tsarin zabe.

Duk da cewa ba su yi tsokaci kan yiwuwar sanya takunkumin ga kasar ba tukuna, amma sun nuna yiwuwar daukar mataki ga wadanda ke kawo cikas ga aiwatar da matakan da aka tsara.

Ana sa ran wani sabon manzon ECOWAS zai tafi Bissau a cikin kwanaki masu zuwa don ganawa da shugabannin gwamnatin mulkin soja.

A Jiya Lahadi ne shugabannin kungiyar ta ECOWAS suka gudanar da taronsu karo na 68 a Abuja fadar mulkin Najeriya.

Taron na wannan karon ya ne a daidai lokacin da ake fama da juyin mulki a tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Na baya baya nan shi ne yunkurin juyin mulin a Benin, sai wanda ya yi nasara a karshen watan jiya a Guinea Bissau.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted