Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa Birtaniya, Faransa da Jamus suna shirye-shiryen mayar da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran a shekarun baya.
Kasashe uku na Turai, da aka fi sani da E3, sun gana da jami’an Iran a ranar Talata a wani abin da aka bayyana a matsayin dama ta karshe na ceto huldar da ke gabansu na yin amfani da batun yarjejeniyar nukiliyar 2015, wanda wa’adinsa zai kare a tsakiyar watan Oktoba.
Duk da cewa jami’an diflomasiyyar Turai sun yi iƙirarin cewa tattaunawar ba ta samar da hanyoyin warware batun kamar yadda suke bukata ba, amma Tehran ta nanata cewa tana nan a shirye don tattaunawa mai ma’ana, muddin aka mutunta haƙƙinta da kuma kawar da duk wata barazana daga waje.
E3 na shirin ƙaddamar da matakan ne mai yiwuwa daga wannan Alhamis. Wadannan takunkuman dai za su sake shafar muhimman harkokin kudi, makamashi, hada-hadar bankuna, da kuma bangaren tsaro na Iran, lamarin da zai kara yin tasiri ga tattalin arzikin kasar.
Kamar yadda wani jami’in diflomasiyyar kasashen yammacin duniya ya yarda, “Za a fara tattaunawa kan batun da zarar an mika wasikar (ga kwamitin sulhu na MDD).
Berlin ta tabbatar da cewa wannan batu yana kan nazari, yayin da London da Paris suka yi gum da bakunansu. A nata bangaren, Tehran ta bayyana karara cewa za ta mayar da martani mai tsauri idan aka kakaba mata takunkumi, wanda ke nuni da matakin da ta dauka na kin mika kai ga matsin lamba na bai daya.