Duniyarmu A Yau : Taron Kasashen Kungiyar D-8 Karo Na 11 A Masar

A ranar laraba ne aka bude taron kasashen masu tasowa 8 daga cikin kasashen musulmi wato D-8 a birnin Alkahira na kasar Masar, wacce ta

Kungiyar D-8 A Masar

A ranar laraba ne aka bude taron kasashen masu tasowa 8 daga cikin kasashen musulmi wato D-8 a birnin Alkahira na kasar Masar, wacce ta karbi shugabancin kungiyar na shekara mai zuwa.

Kasashe mambobi a kungiyar D-8 dai sun hada da Masar, Turkiyya, Iran, Najeriya, Bangladesh, Pakista, Indonasia da Malasiya. An kasa kungiyar a shekara 1997 a birnin Istambul na kasar Turkiyya, kuma a nan ne cibiyar kungiyar take.

Taron shuwagabannin kungiyar D-8 na farko, an gudanar da shi ne a birnin Istambul na kasar Turkiya a shekarar da aka kafa kungiyar, sannan shuwagabannin kasashe 3 ne suka sami damar halattan taron kungiyar na farko daga ciki har da marigayi shugaban kasar Iran na lokacin Sheikh Hashin Rafsanjani. Ya zuwa yanzu kungiyar ta gudanar da tarurruka har 10, wannan shi ne na 11th.

Manufar kafa kungiyar D-8 dai sun hada da raya kasashen na musulmi 8 da sauran kasashen musulmi a fagege daban –daban, wadanda suka hada da tattalin arziki zamantakewa, da siyasa da sauransu.

Taron Alkahira dai shi ne taro na 11 wanda shuwagabannin kungiyar suka halatta don tattauna matsaloli da kuma hanyoyin warwaresu, har ila yau da kuma samun cikekken rahotomdangane da agendojinsu na baya, da kuma inda aka tsaya don wajen aiwatar da su.

Kungiyar tana da babban sakatare wanda yake gudanar da harkokin kungiyar da kuma ganin an aiwatar da dukkan al-amuran da kungiyar amice a gudanar da su. Akwai kwamitoci da dama a cikin kungiyar wadanda suka hada da na ilmi da ci gaba, wanda a karkashinsa suke da Jami’a ta kimiya da fasaha na kungiyar D-8 a birnin Hamedan na JMI, Jami’ar wacce take gina karatunta a kan bincike, yana bada digiri na biyu, wato Masters da kuma digiri na Uku wato Phd duk bisa bicnike da kuma aiki a kasa.

Banda haka D8IU yana hulda da wasu zababbuna manya-manyan Jami’o’i a cikin kasashe mammbobi a kungiyar don samun musayar ilmi da kuma aiki tare don ci gaban wadannan kasashe.

A halin yanzu dai Ambassador Isiaka Abdulqadir Imam daga tarayyar Najeriya ne babban sakataren kungiyar, kuma yana da wasu mataimaka a kwamitoci daban-dan a na kungiyar.

Masoud Pezeskiyan shugaban kasar Iran a jawabinda ya gabatar a safiyar Alhamis a taron kungiyar na 11TH ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta gina harsashe na samar da Bankin D-8 saboda ci gaban kasashe mambobi a cikinta.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana muhimmancin aiki tare na kasashen kungiyar don bunkasa tattalin arzikinsu, ya kuma yi kira ga kasashen su yi aiki tare a bangarori daban-daban don kara saurin bunkata tattalin arkin kasashen. Musamman a dai-dai lokacinda kasar Masar take jagorantar kungiyar, a jagorancin karba-karba.

Shugaban yace yana fatan kasar Masar zata yi kokarin ta samar da ci gaban a zo a gani a lokacinda take jagorancin kungiyar da kuma aiki tare a bangarori daban daban a cikin kasashe mambobi a cikinta.

Dangane da matsalolin tsaro a yankin gabas ta tsakiya kuma, shugaban ya yi allawadai da yakin da HKI taje jagoranta a Gaza, fiye da watanni 14 da suka gabata, da kuma abinda take yi na mamayar karin yankuna a kasar Siriya da kuma hare-haren da take kaiwa kasashen Lebanon da kuma Yemen.

Ya ce, sojojin gwamnatin HKI suna ci gaba da kissan falasdinawa maza da mata da yara, wadanda yawansu a halin yanzu ya wuce 45,000. Kuma mafi yawan wadanda suka kashe kuma suke ci gaba da kashewa mata da yara ne, wadanda basa dauke da makami.

Shugaban wa wani wuri a jawabinda ya ce, abinda HKI take yi a gaza ya sabawa dukkan dokokin kasa da kasa da suka hana irin wannan kissan kare dangi. Sannan ya bukaci hadin kan kasashen musulmi don fuskantar wadannan ayyukan ta’addanci wanda HKI da kawayenta Amurka da kasashen yamma suke tallafawa. Yace, hadin kan musulmi ne kawai zai iya kawo karshen halin da wasu kasashe a yankin suke ciki.

Har’ila yau a wani bangare na jawabinda shugaba Pezeshkiyan ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen na D-8 su kafa asusun ci gaba na kungiyar wanda zai tara kudaden jari na ko wace kasa daga cikin kasashen kungiyar, wanda kuma zai zama ginshikin harkokin kasuwanci tsakanin kasashen 8.

Yace kasar Iran , a namma a shirye take ta jagoranci kafa wannan asusun ta zaba jari da kuma kungiyar ta D-8. Yace kungiyar D-8 wata babbar kasuwa ce ga kasashen kungiyar, don haka wata dama ce ta habaka tattalin arzikin kasashen gaba daya.

Daga karshe ya tunatar da shuwagabannin kasashen kungiyar da kuma wakilansu kan cewa, cika alkawali yana da matukar muhimmanci a musulunci, don haka yakata duk abinda kungiyar ta amince ta kuma tsaya a kai, to a tabbatar da cika alkawari an kuma aiwatar da shi kamar yadda ya dace.

Babban sakataren kungiyar farfesa Abdulkadir Imam, a maida martani ga shawarorin da shugaba Masoud Pezeskiya na JMI ya gabatar, ya gede masa., ya kuma yi fatan, sauran kasashen kungiyar zasu taimaka don ganin an tabbatar da wadannan shawarori.

Sannan ya yabawa JMI kan irin rawar da take takawa a ci gaban kungiyar tun lokacin kafata ya zuwa yanzu. Ya yi kira ga kasashen kungiyar su amfani da irin ci gaban da kasar Iran take da shi a bangarorin ilmi da dama. Ya bukaci yan kasuwan kasar Iran su yi amfani da wannan damar don samun kasuwa a cikin mutane kimani biliyon 1.2 da kungiyar take da su.

A ziyarar da ya kai birnin Alkahira na kasar Masar, don halattan taron na D-8 shugaban Pezeskiyan ya hadu da shuwagabanni da kuma manya-manyan jami’an gwamnatocin sauran kasashen kungiyar.

Banda haka ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ta D-8 wanda aka gudanar a birnin na Al-kahira kwana guda kfin taron shuwagabannin kasashen.

Shi ma a ganawarsa da tokwarorinsa na kasashen kungiyar Abbas Aragchi ya gana da Hakan Fidan ministan harkokin wajen kasar Turkiyya, inda suka tattauna sabban al-amura da suke faruwa a yankin Asia ta kudu, tare da maida hankali kan abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya da kuma halin da ake ciki a Gaza.

Manya-manyan Jami’an diblomasiyyar kasashen  biyu sun jaddada bukata da kuma muhimmancin manya –manyan kasashen musulmi musamman kasashen D-8 na hada karfi da karfe don kawo karshen ta’asan da HKI take aikatawa a cikin kasashen musulmi, musamman a zirin gaza, Lebanon da kuma Siriya.

Babban agenda taron kungiyar D-8 karo na 11th wanda aka gudanar a ranakun 11-12 ga watan na watan Decemban shekara ta 2024 dai shi (Zuba jari Matasa da kuma tallafawa kanana da matsakaitan kamfanoni na kasashen kungiyar)

A nashi jawabin shugaban kasar Masar kuma mai masaukin baki, har’ila yau shugaban karba-karba na taron D-8 karo 11th Abdulfattah Assisi, ya ce: Gabas ta tsakiya tana fuskantar matsaloli masu yawa kuma masu sarkakiya. Sannan akwai yiyuwan watan yaki a yankin ya kara yaduwa zuwa wasu kasashen yankin, banda kasashen da ake yaki a cikinsu a halin yanzu.

Tashar talabijin ta Aljazeer Mubashir ta kasar Qatar ta nakalto Assisi yana cewa, rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya a halin yanzu bai taba kaiwa irin munin da ya kai.

Yakin da HKI ta ke yi a Gaza, tun watanni 14 da suka gabata, sun sabawa dokokin kasa da kasa, Kuma kamar yadda kowa ya san abinda ya faru a kasashen Lebanon da Siriya, akwai yiyuwar wannan yakin da ke faruwa a Gaza, ya yaduwa zuwa wasu kasashe na yankin.

Shugaban ya yi allawadai da mamayar da sojojin HKI suka yi kuma suke kara mamayar kasar Siriya, ya ce wannan ma, yana kara nuna cewa, yakin nan zai kara zafi da tsanani nan gaba.

Ya ce, kasar Siriya kasashe wacce take da yencin kanta, kuma dole ne a mutunta yencin ko wace kasa, don haka abinda HKI take yi a kasar Siriya ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Masana suna ganin idan shuwagabanin kungiyar D-8 sun cika alkawulansu wadanda suka amince a tarurrukan da suka gabata a baya, kungiyar tana iya zama babban kungiyar wacce zata raya kasashen musulmi da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments