Duniyarmu A Yau: Dangantakar Tattalin Arziki Tsakanin Rasha Da Iran

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ;Duniyarmu a Yau’ shiri wanda yake kawo maku labarai masu

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na ;Duniyarmu a Yau’ shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi tattalin arziki, tsaro zamantakwa da sauransi. Inda muke masu karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan shirin.

///… Masu sauraro shirimmu nay au sai yi Magana ne danda da ‘yaki tsakanin gwamnatin kasar Siriya da kuma yan ta’adda wadanda suke iko da wasu yankunan kasar Siriya tun shekara ta 2011 tare da taimakon kasashen yamma da kuma wasu kasashen yankin daga ciki har da kasar Turkiyya.

A shekara ta 2011 ne yan ta’adda wadanda gwamnatocin kasashen yamma musamman Amurka suka samar suka farwa kasashen Iraki da Siriya, inda suka kafa daularsu wacce ta hada bangaren mai yawa na kasar Iraki da kuma bangare masu yawa na kasar Siriya.

An yi wani lokaci wanda, yan ta’adda a kasar siriya, wadanda wadannan kasashe, da kuma wasu daga cikin kasashen yankin suke kira “Masu adawa da gwamnatin shugaban Bashar Al-Asad’ sun mamaye dukkan kasar Siriya sai abinda baifi kashi 20% ba. Wato, a lokacin ba abinda ya ragewa gwamnatin kasar Siriya sai birnin Damascus babban birnin kasar kadai.

Amma tare da taimakon kawayenta, wadanda suka hada da kasashen Iran da Rasha, da kuma kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin Asiya ta kusu, wadanda suka hada da Hizbullah na kasar Lebanon da kuma Hashdushabi na kasar Iraki, suka hada karfi da karfe suka kwace kasar Iraki daga hannun kungiyar yan ta’adda ta Daesh. Sannan a kasar Siriya kuma sun dawo da ikon gwamnatin kasar, a kan mafi yawan kasar,  karkashin shugabancin Bashar Al-Asad, in banda arewa maso gabacin kasar, inda kasar Amurka ta kafa sansanin sojojinta a yankin tana satar danyen man fetur da kayakin guna na mutanen kasar ta Siriya tana kuma taimakawa wasu kungiyoyin yan ta’adda wadanda take taimakwa.

Banda haka gwamnatin Urdugan na kasar Turkiya ma tana goyon bayan wata ko wasu daga cikin kungiyoyin yan ta’ada wadanda suke don kifar da gwamnatin shugaba Bashar Al-Asad, sannan ta mamaye wani bangare na kasar ta Siriya inda bar yan ta’addan suna harkokinsu a yankin.

Wannan ya dauki shekara kimani 4 kafin dakarun kawancen gwagwarmaya a yankin su sami nasara a kan wadannan yan ta’adda.  Don haka tun lokacin ne, wato tun shekara ta 2017 ne yan ta’addan nan tare da taimakon kasashen Amurka da HKI da kuma Turkiyya suke cikin karensu ba babbaka a yankin.

Amma bayan an tsagaita budewa juna wuta tsakanin kungiyar Hizbullah, ta kasar Lebanon da kuma HKI, bayan yaki na kimani watanni 14, a ranar laraba ta sama wato, 27 ga watan Nuwamban da ya gabata, sai yan ta’adda, musamman wacce ake kira ‘Hai’atu Tahrirul Sham’ ko kuma wacce ake kira ‘Jibhatun Nasra a baya, ta farwa garin Halab na kasar Siriya wanda yake karkashin ikon gwamnatin kasar Siriya suka mamaye, wasu yankuna a cikin birnin, daga ciki har da wasu cibiyoyi masu muhimmanci, wadanda suka hada da barikin sujojin da suke cikin birnin.

A jawabin da ya gabatar a gaban kwamitin tsaro na MDD bayan yaki ya sake tashi a kasar Siriya tsakanin wadannan kungiyoyi da kuma sojojin kasar, jakadan kasar Siriya a MDD Kusai Dhahhak, ya bayyana cewa kwamitin tsaro na majalisar kan cewa,  yawa da kuma fadin yankunan da mayakan yan ta’adda suka mamaye daga birnin Halab na kasar Siriya da daren ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata, ya tabbatar da cewa, kasashen wajen suna da hannu a cikinsa, musamman kuma gwamnatin HKI, Turkiyya da kuma Amurka.

Dahhak ya kara da cewa, ganin irin makaman da wadannan yan ta’adda suka yi amfani da su a hare-haren daren 27 ga watan Nuwamba, ya nuna cewa, basu kai wadan nan hare-hare da radin kansu ba, sai dai da yardarm HKI wacce take kaiwa kasar Siriya hare-hare kusan a ko wace rana a wasu lokuta. Har’ila yau dolene, sun sami izinin gwamnatin kasar Turkiyya wacce take taimaka masu a duk tsawon wadannan shekaru, da kuma gwamnatin kasar Amurka.

Dahhak ya kara da cewa, wadannan kasashe sun yi amfani da kungiyar yan ta’adda wacce ake kira ‘Hai’at Tahriru Sham ne’ don kifar da gwamnatin kasar Siriya, saboda taimakawa HKI da Amurka su kai ga manufofinsu a kasar.

Jakadan ya kara da cewa, lokacinda mayakan yan ta’addan suka zaba don kwace wasu yankuna na birnin Halaby a nuna cewa gwamnatin HKI tana da hannun a cikin ayyukan yan ta’addan, don ta rage zafin shan kaye da kaskancin da ta dauka  a hannun dakarun Hizbulla na kasar Lebanon. Kuma manufar wadannan kasashe ta karshe ita ce, ganin faduwar gwamnatin kasar Siriya, ko gwamnatin shugaan Bashar Al-Asad wacce ta kasance cikin kasashe wadanda suke cikin kawancen kasashe masu gwagwarmaya da mamayar da HKI takewa kasashen larabawa.

Saboda muhimmancin wannan al-amarin da kuma hatsarinsa, Janar Mohammad Bakiri babban kwamandan sojoji JMI ya zata ta wayar taro da, Andru Blosov babban kwamandan sojojin kasar Rasha a Siriya, da babban kwamdan sojojin kasar Iraki Janar Yarallah, Janar Abdulkarin babban kwamandan sojojin kasar Siriya, inda ya tabbatar masu cewa akwai wani makirci a wannan al-amarin don haka dole ne su fara daukar matakan da suka dace don hana wadannan yan ta’adda rikita yankin da wani sabon yaki.

Janar Bakiri ya kara da cewa: Hare-haren yan ta’addan a dai dai lokacinda aka dakatar da bude wuta tsakanin Hizbullah da kuma HKI, ya nuna cewa akwai wata kulalliya ga kasashen yankin wanda HKI da kuma Amurka suka saka.

Kuma sun yi haka ne don tabbat da cewa kasashen Siriya da kawayenta a yankin sun yi rauni, ta yadda ba zasu yi tunanin fadawa HKI da yaki ba, musamman bayan sun tabbatar da cewa sojojin HKI sun sha wahala kuma sun cikin rauni mafi muni a tarihin haramtaciyar kasar bayan fafatawa da dakarun Hizbullah na kasar Lebanon.

Har’ila yau jakadan kasar Siriya a MDD Kusai Dhahhak, ya bayyana cewa a hare-haren da yan ta’adda na ‘Hai’at Tahriru Sham suka kai kan birnin Halab, wanda suka suka watsa hotunansu a lokacinda suka shiga garin, ya nuna cewa gwamnatin kasar Turkiya tana da hannu, wajen tallafa masu, da makamai daban daban masu hatsari wadanda suka hada da jiragen yaki masu kunan bakin waje, kuma na zamani, da motocin yaki da makamai masu wargaza tankunan yaki da sauransu.

Har’ila yau a hotunan an nuna yan ta’addan suna kafa tutocin kasar Turkiya a kan gine-ginen gwamnati da suka kwace.

Wani dan jarida mai sharhin labarai, Abdul-Bari Atawa, wanda kuma yake da jaridar Arra’ayul Yaum, ya bayyana a cikin jaridarsa dangane da abubuwan da suke faruwa a Siriya kan cewa, hare-haren da dakarun kungiyar yan ta’adda ta Hai’at Tahriru Sham ( ko Jibhatun Nusra a da) suka kai kan kasar Siriya a ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata, ta yi shi ne tare da sojojin kasashen waje a cikinsu. Ya kuma kara da cewa: wadannan hare-hare ban a ba zata bane, sai dai kasashe makiya gwamnatin kasar Siriya ce suka shirya shit un da dadewa. Kuma duk wanda ya san siyasar yankin gabas ta tsakiya, ya san cewa gwamnatocin kasashen Turkiyya, Amurka HKI ne suka shirya wadan nan hare-hare kuma sune suka bawa yan ta’addan duk kayakin aikin da suke bukata don kaddamar da wannan harin a kan kasar Siriya.

Banda haka an shirya wadannan hare-haren ne watanni da dama kafin a kaisu, kuma masana da dama suna ganin a cikin yankuna da yan ta’addan suke iko da su, akwai dakuna na karkashin kasa wadanda sojojin da kwararru na wadannan kasashe suke gudanar da harkokin yakin kan kasar Siriya.

Amma labaran da suke fitowa daga bangaren gwamnatin kasar Siriya da kuma sojojin kasar sun bayyana cewa, sojojin kasar sun sake girka sojojinsu a wajen birnin Hamah, don kada su sake shigowa birnin ko kuma yakin ya hada da fararen hula.

Majiyat sojojin ta bayyana cewa, a cikin yan kwanakin da suka gabata sun shiga yaki mai tsanani da yan ta’adda wadanda suke amfani da manya –manayn makamai da kuma jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa masu yawa.

Majiyar sojojin kasar ta Siriya ta bayyana a yau Alkhamis kan cewa, zasu yi abinda ya zama wajibi a kansu na kare kasar Siriya daga makiyanta a matsayinsu na yan kasa. Zasu ci gaba da kokarin fitar da yan ta’adda daga yankunan da suka kwace daga hannun gwamnatin kasar Siriya a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Labarin ya kara da cewa, yan ta’addan sun yi amfani da makaman zamani, musamman jiragen yakin da ake sarrafasu daga newsa kuma masu kunan bakin wake. Amma duk da haka sun kashe kimani 300 daga cikinsu.

Majiyar ta kara da cewa sojojin sun sami nasarar fatattakar, mayakan yan ta’addan na musamman wandanda ake kiransu “Al-Asa’ibul Hamra’ a wani tarkon da suka kafa masu suka kuma fada cikinsa.

Labarin ya kara da cewa wannan ya faru ne a tsaunuka, Zainul Abideen’. Kuma yakin da suka yi a ‘Jabal Zainul Abideen’ ya dauki dukkan tsawon daren ranar Alhamis, wannan kuma duk tare da cewa yan ta’adan sun yi amfani da jiragen yaki masu kunan bakin wake.

Amma a bangaren siyasa a ranar Jumma’a ce aka gudanar da taro tsakanin jami’an tsaron kasar Iraki da Iran, a birnin Bagdaza don sanin matakan da zasu dauka dangane da yakin na Siriya.

Har’ila yau a makon mai zuwa ne ake saran kwamitin “astana na samar da zaman lafiya a kasar siriya’ zai gudanar da taro don tattauna wannan batun.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alikum warahmatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments