Search
Close this search box.

Duniya ta yi kira da a dauki mataki bayan kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a Rafah

A yammacin jiya Lahadi ne sojojin mamaya na yahudawan Isra’ila suka sake yin wani sabon kisan kiyashi kan wasu da dama daga cikin ‘yan gudun

A yammacin jiya Lahadi ne sojojin mamaya na yahudawan Isra’ila suka sake yin wani sabon kisan kiyashi kan wasu da dama daga cikin ‘yan gudun hijira ta hanyar jefa bama-bamai a tantunan da aka kafa a rumfunan adana kayayyaki na UNRWA da ke Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Jami’an gwamnati da cibiyoyin kasa da kasa sun yi gaggawar yin Allah wadai da kisan kiyashin, tare da yin kira ga “Isra’ila” da ta dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa.

Kamfanin dillancin labaran Wafa ya habarta cewa, mai magana da yawun shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi tir da harin da Isra’ila ta kai kan Tal-Sultan a matsayin wani kisan gilla da ya wuce dukkan iyakoki da ka’idoji na kasa da kasa.

Nabil Abu Rudeineh “ya jaddada bukatar gaggauta shiga tsakani domin dakatar da laifukan da Isra’ila take aikatawa kan al’ummar Palasdinu nan take” ya kuma kira “mummunan kisan kiyashi” a matsayin kalubale ga umarnin kasa da kasa da suka hada da “hukuncin kotun kasa da kasa (ICJ). ) da ta umurci  Isra’ila da ta dakatar da hare-haren soji a kan birnin Rafah da kuma ba da kariya ga al’ummar Palasdinu.”

Abu Rudeineh ya dora alhakin hakan a kan  gwamnatin Biden dangane da laifukan Isra’ila, yana mai kira ga Washington da ta “tilasata Isra’ila ta dakatar da kisan kare dangi da take aikatawa a Gaza.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments