Kasashen duniya sun fara aikewa da sakon taya Lebanon murna kan samun sabon shugaban kasa.
Faransa ta aike da sakon taya murna ga Joseph Aoun, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar, a wani lokaci mai matukar muhimmanci ga makomar kasar, a cewar ma’aikatar harkokin wajen kasar.
A cikin wata sanarwa da Quai d’Orsay ta fitar ta ce “Dole ne a yanzu a yi nadin wata gwamnati mai karfi, mai goyon bayan shugaban kasar, mai iya hada kan ‘yan kasar Lebanon, don amsa bukatunsu.” .
Emmanuel Macron da kansa ya aika “taya murna” ga sabon shugaban Lebanon, Joseph Aoun a kan shaffin X.
Shi ma Ofishin jakadancin Amurka a Lebanon ya bayyana cewa ya kuduri aniyar yin aiki kafada da kafada da sabon shugaban kasar Joseph Aoun.
“Mun kuduri aniyar yin aiki kafada da kafada da shugaba Aoun yayin da yake fara kokarinsa na hada kan kasar, aiwatar da gyare-gyare da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga Lebanon,” in ji ofishin jakadancin a X.
Isra’ila ma ta ‘ taya kasar Lebanon smurna aboda zaben sabon shugaban kasar.
Ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce yana taya kasar Labanon murnar zaben shugaban sojojin kasar Joseph Aoun a matsayin shugaban kasa.
“Ina fatan wannan zabi zai taimaka wajen samun kwanciyar hankali, kyakkyawar makoma ga Lebanon da al’ummarta da kuma kyakkyawar dangantakar makwabtaka,” Saar ya rubuta a cikin wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta.