Dubban Mutane Ne Suka Taru Don Tunawa Da Kwanaki 40 Da Jana’izar Jagora

a nan tehran ne aka yi taron tunawa da cika kwanaki 40 da jana'izar jagoran juyin musulunci

Dubun dubatan mutane ne dauke da jar tuta ta daukar fansa da tutoci dake dauke da hoton tsohon jagora suka taru a babban masallacin jumaa na Imam Khumaini dake nan birnin Tehran domin tunawa da zagayowar  kwanaki 40 da jana’izar jagaron juyin musulunci na kasar Ayatullah sayyid Ali khamna’I da yayi shahada sakamakon hari da Amurk da isra’ila suka kai masa a gidansa, inda suke ta rera taken tabbar da adalci da kuma ci gaba da bin hanyarsa ta gwagwarmaya da makiya

An gudanar da gagarumin taron ne acikin yanayin na bakinci da juyayi wanda jagoran juyin musulunci na iran Ayatulla sayyid Mujtaba khamana’I ya gayyaci mutane ,mahalartar taron sun cika masallacin fal, kuma suna ta rera taken neman daukar fansar jagoran kan wadanda suka kashe shi,

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin kasar da suka kunshi bangaren siyasa dana soji, kamar shugaban kasa Mas’ud pezeshkiyan da kuma mataimakin shugaban kasa na farko mohammad redha Arif, da shugaban majalisar shawarar musulunci mohammad Qalibaf da kuma alkalin alkalai na kasa Ghulam Hussain muhsen Eji .

Kuma ana saran gudanar da irin wannan zaman makoki din a ranar Alhamis mai zuwa da yamma a hubbaren sayyida fatima ma’asuma dake birnin qum kanwa ga limami na 8 daga cikin limaman shiriya 12 wato Imam ridha As.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted