Dubban ‘yan Mexico ne suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar, domin nuna adawa da yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza.
A yammacin wannan Lahadi, masu zanga-zangar sun daga tutocin Falasdinu tare da daukar da tutoci da kwalaye masu dauke da sakonnin nuna adawa da Isra’ila.
Sun yi ta rera taken nuna adawa da saka al’ummar Gaza a cikin yunwa da gangan da hakan ya shafi kananan yaran Falasdinawa da ke Gaza, tare da jaddada wajabcin magance matsalar jin kai cikin gaggawa da ta addabi yankin.
Lamarin dai na da nasaba da bacin rai da nuna bakin ciki, kan ayukan kisan kiyashin da Isra’ila take aikatawa a Gaza, inda masu jawabi suka bayyana irin mawuyacin halin da farar hula ke ciki zirin Gaza.
Mahalarta zanga-zangar sun yi kira da a gaggauta shiga tsakani na kasa da kasa don dakatar da kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa fararen hula tare da neman ba da izinin shiga cikin yankunan da aka yi wa kawanya ba tare da wani shaharadi ko takura ba.
Mutane da dama sun yi na’am da bukatar mayar da martani a duniya game da rikicin, tare da yin kira ga kasashen duniya da su kara daukar kwararan matakai kan wuce gona da iri na Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Masu zanga-zangar sun bukaci da a kakabawa jami’an Isra’ila takunkumi a duniya da kuma dakatar da huldar kasarsu da gwamnatin Tel Aviv.
Bugu da kari, sun yi kira da a hukunta jami’an gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila kan laifukan da suka aikata a Gaza da sauran wurare a yankin.